Zanga-zanga a Senegal
February 19, 2012'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Dakar babban birnin kasar Senegal ranar asabar, a daidai lokacin da jami'an tsaro ke kammala kada kuri'un su a zaben shugaban kasar da ke tattare da sarkakiya.
Wannan na zama wuni na hudu da ake zanga-zanga, gabanin zaben na mako mai zuwa inda shugaban kasa Abdoulaye Wade mai shekaru 85 da haihuwa zai tsaya takara da 'yan adawa sha uku wadanda ke neman ganin shugaban ya mika ragamar mulkin kasar
A jiya asabar Jami'an tsaron kasar masu yawan dubu 23 da ma 'yan sanda, suka fito su kada nasu kuri'ar da wuri. Tawagar kungiyar Tarayyar Turai wadda ta sanya ido a zaben ta ce takardun zaben sun iso a kan lokaci kuma an gudanar da zaben cikin lumana.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Saleh Umar Saleh