Zanga zanga a Tanzaniya
January 6, 2011Mutane Guda biyar suka rasa rayukansu yayin da wasu a ƙalla guda 60 suka samu raunika a birnin Arusha da ke a arewacin ƙasar Tanzaniya. A sa'ilin wata zanga zanga ta 'yan adawa kamar yadda wani jami'in jam'iyyar hamayya mafi girma ta ƙasar wato Chadema John Mrema ya shaidawa kamfanin dilancin labarai na Faransa AFP.
Rahotanin dai na karo da juna akan wannan labari da yan sandar suka ce mutane biyu kwai ne suka mutu yayin da wasu guda tara suka jikata. sannan kuma sun ce sun kama mutane kamar guda 50 menba na ƙungiyar ta Chadema a cikin hada Wilbrod Slaa jagoran yan dawar da ya tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a cikin watan oktoban da ya gabata.
Mista Merema wanda ya ce har a safiyar yau 'yan sandar na ci- gaba da kame yan adawar ya baiyana cewa ya na da wahala kawo yanzu a haƙiƙance yawan jama'ar da ke cikin hannu jami'an tsaron.
Duban jama'ar magoya bayan jam'iyyar adawa ta Chadema sun gudanar da zanga zanga ne domin yin Allah wadai da sake zaɓen da aka yi wa Jakaya Kikiwete a masayin shugaban ƙasar wanda suke zargin gwamnatin sa da cin hanci.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu