Zanga-zanga a wajen taron muhalli a birnin Montreal na Kanada
December 4, 2005Talla
Dubun dubatan mutane sun gudanar da zanga-zanga a gun babban taron muhalli na duniya dake gudana a birnin Montreal na Kanada don yi kira da a dauki sahihan matakan rage dumamar yanayi a duniya baki daya. Wadanda suka shirya zanga-zangar da aka yiwa taken macin kare yanayin duniya sun ce mutane kimanin dubu 40 suka fita kan titunan birnin na Montreal don yin wannan maci. Kungiyoyi 25 ciki har da masu fafatikar kare muhalli da kungiyoyin ma´aikata da na dalibai suka shirya zanga-zangar. A ranar litinin da ta gabata aka bude taron na makonni biyu a birnin na Montreal. Kimanin wakilai dubu 10 daga kasashe kusan 190 ke halatar taron dake tattaunawa akan matakan da za´a dauka wajen rage dumamar doron kasa da kuma yadda za´a tinkari yarjejeniyar birnin Kyoto.