Kungiyoyi a Sudan sun zargi shugaban kasar Masar
April 26, 2019Talla
Al'ummar kasar dai na amsa kiran kungiyoyin masana wadanda suka yi zaman dirshan tun bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir da sojojin sukayi, ciki kuwa harda rukunin alkalan kasar ta Sudan wadanda masu zanga-zangar su kayi yunkurin korar su tun da fari sakamakon zargin bangaren shari'a da marawa tsohon shugaba al-Bashar baya.
A makon daya gabata shugabannin kasashen Afirka suka gudanar da taron gaggawa kan rikicin kasar ta Sudan inda suka ba sojojin wa'adin mika mulki ga farar hula matakin da ya kara tunzura masu zanga-zangar a halin yanzu.