Zanga-zangar ranar juyin mulki a Sudan
October 25, 2022Talla
Zanga-zangar ta Sudan na zuwa ne a daidai lokacin da Sudan ke bikin cika shekaru guda da aiwatar da juyin mulki da babban hafsan sojan kasar Janar Abdel Fattah al-Burhane ya yi, bayan da karya dukkan alkawurran da ya dauka shekaru biyu da suka gabata.
A cikin shekara guda dai, masu zanga-zanga 118 ne suka mutu, sakamakon fafutkar da suka yi wajen neman tabbatar da dimokuradiyya, da ke zama sharadi daya tilo da kasashen waje suka gindaya wajen maido da agajin kasa da kasa da ya katse.
Yanayin tattalin arzikin kasar da ke zama daya daga cikin mafi talauci a duniya ya shiga cikin wannan mummunan hali, inda hauhawar farashin masarufi da barazanar 'yunwa ke shafar miliyoyin mutane a kasar.