Zanga-zanga a Amirka bayan kisan Geroge Floyd
June 4, 2020Zanga-zanga ta barke a birane da dama na kasar Amirka bayan mutuwar George Floyd wani bakar fata biyo bayan azabar da wani dan sanda ya gana masa bayan kama shi a birnin Minneapolis.
Amirkawa manya da kanana, daga rukunnan al'umma dabam-dabam sun fantsama a saman titunan biranen kasar inda zanga-zangar ta rikide zuwa bore da ya yi sanadiyyar gudanar da kone-kone da fashe-fashen shaguna da kuma dauki ba dadi da 'yan sanda. Lamarin da ya kai Shugaban Donald Trump daukar matakin fito da sojoji domin taimaka wa 'yan sanda murkushe zanga-zangar da ta ki ci ta ki cinyewa.
Sai dai matakin amfani da karfi da hukumomin Amirka suka yi ya fuskanci suka daga kasashen duniya musamman na Turai da ma Afirka. Wannan ya kai ga yaduwar zanga-zangar zuwa wasu kasashen duniya domin kawo goyon bayan da zanga-zangar Amirkawan da kuma nuna adawa da tabi'ar kisan bakar fata a kasar ta Amirka.