Zanga-zangar adawa da manufar Erdogan
November 12, 2016Talla
Zanga-zangar dai wasu 'yan asalin kasar ta Turkiya da ke zama a kasar Jamus, wadanda suka hada da Kurdawa suka shirya ta, inda suke dauke da hotunan shugaban kungiyar Kurdawa ta PKK Abdallah Ocalan. A cewar masu zanga-zangar matakan kame mutane da gwamnatin Erdogan ke yi a yanzu, tun bayan yunkurin juyin mulki, lamarin ya zarta misali, inda ake kama duk mai adawa da gwamnati da kuma hana kafafen yada labarai yin ko wane irin sukar da ta shafi gwamnati.