1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da takarar shugaba Wade a ƙasar Senegal

January 28, 2012

Wata zanga-zanga ta turnuƙe titunan Senegal bayan wani hukunci da kotun kolin ƙasar ta yanke game da zaben ƙasar mai zuwa.

https://p.dw.com/p/13sKB
Senegalese police confront an opposition supporter in the Medina neighborhood of Dakar, Senegal, Saturday, Jan. 27, 2007. Riot police fired tear gas at protesters calling for early parliamentary elections Saturday, beating back the crowd with rifle butts and detaining the head of the country's main opposition party. (AP Photo/Rebecca Blackwell)
Jami'an tsaro sun tsare wani mai goyon bayan 'yan adawaHoto: AP

Tun a daren Juma'a alummar Senegal ta shiga zanga-zanga a titunan kasar bayan da babban kotun ƙasar ta yanke hukuncin cewa shugaba mai ci Aboulaye Wade zai iya tsayawa takara domin neman wa'adinsa na uku a kan kujerar mulkin kasar.

Gidan talabijin na cikin gida ya rawaito cewa dan sanda guda ya mutu a babban birnin kasar wato Dakar bayan da ya sami raunaka a kansa.

Abokan hammayan shugaba Wade mai shekaru 85 da haihuwa sun ce bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar wa'adi biyu ya dace shugaban ya yi a mukamin, kuma ya riga ya cika su. To sai dai Wade wanda ya fara mulkin kasar a shekara ta 2000 ya bayar da hujar cewa bai kamata a sa wa'adin sa na farko a cikin lissafi ba.

Majalisar kolin kasar ce ta amince da takarar shugaba Wade da na abokan hammayarsa guda 13 a zaben da ake sa ran gudanarwa ran 26 ga watan Fabrairu mai kamawa, To sai dai ta ki ta amince da takarar mawakin nan mai suna Yossour Ndour wanda ta ce bai sami goyon bayan mutane dubu 10 ba bisa tanadin dokar kasar.

Senegal ce kadai kasar da bata yi fama da juyin mulki ba tun bayan da ta sami 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka. A yanzu haka dai zaben na watan gobe na zaman wani zakaran gwajin dafi ga dorewar zaman lafiya da zamantakewa a kasar.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita:           Mohammad Nasiru Awal