1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da taron muhallin Paris

Gazali Abdou TasawaNovember 29, 2015

Daruruwan masu adawa da taron muhalli na duniya da zai gudana daga Litinin sun gudanar da zanga-zanga a Paris domin matsa lamba ga shugabannin kasashen duniya

https://p.dw.com/p/1HEPo
Paris Anti Klimawandel Demonstration Place de la Republique
Hoto: Reuters/PE. Gaillard

Masu zanga-zangar sun gudanar da ita duk da matakin da hukumomin birnin Paris suka dauka na haramta gudanar da ita a bisa dalillai na tsaro. Akasarinsu na sanye da tufafi bakake da kuma kyalle a fuska suna rera kalamai na batanci da kalubalantar matakin hukumomin, suna cewa mulkin danniya ne, ba za mu amince a kwace mana 'yancinmu na yin zanga-zanga ba.

Masu zanga-zangar sun kuma ta jifar 'yan sanda da duwatsu da kuma kwalabe. Su kuma suka yi ta mayar da martani da barkono mai sa hawaye da kuma ruwan zafi.

'Yan sanda sun sanar da kama mutane kimanin 100 daga cikin masu zanga-zangar. Shugabannin kasashe kusan 150 za su halarce taron daga Litinine inda za su yi kokarin cimma wata sabuwar yarjejeniyar rage fitar da gurbattacciyar iska mai lalata muhalli a duniya.