Zanga-zangar goyon bayan jami'an tsaro a Nijar
July 9, 2016Talla
Masu zanga-zangar dai a birnin Yamai, Tahoua, da Damagaram, sun yi ta rera kalammai na nuna adawa ga Boko Haram, da kuma na goyon baya ga jami'an tsaron kasar, inda a birnin na Yamai suka yi jerin gwano kafin daga bisani su tare a harabar majalisar dokokin kasar inda suka gudanar da taron gangami.
Kungiyoyinn fararan hulla ne dai, gami da na kwadago, da kungiyoyin dalibai, suka shirya wannan zanga-zanga wadda ita ce ta biyu da aka shirya a kasar tun bayan da sojojin na Nijar suka tsunduma a cikin yaki da Boko Haram. A farkon watan Yuni ne dai da ya gabata, mayakan na Boko Haram suka hallaka sojojin na Nijar 26 tare da jikkata wasu da yawan gaske a garin Bosso da ke cikin jihar Diffa a Gabashin kasar.