Zanga-zangar sauyin yanayi
Zanga-zanga a daidai lokacin da ake taron kasashen duniya a Spain kan batun muhalli don kammala dokokin fara aiki da yarjejeniyar Paris ta 2015.
Masu nunkaya
Matasa a birnin Berlin na Jamus suna nunkaya a ruwa domin neman ganin an dauki mataki kan sauyin yanayi. An yi zanga-zanga a gaban harabar majalisar dokokin Jamus inda suka nemi a rage fitar da iska mai gurbata muhalli.
Takaicin jan kafa kan muhalli.
Dubban masu zanga-zanga a gaban kofar Brandenburg da ke birnin Berlin na Jamus suna nuna takaicin jan kafa da gwamnati take yi kan samar da matakan kare muhalli. Kimanin mutane 50,000 ne suka shiga wannan zanga-zanga mai taken "Farawa daga farko" domin matsin lamba ga gwamnati kan munufofin kare muhalli.
Nuna ra'ayi
"Yanayi na sauyawa, me zai hana mu?" Tambayar da masu zanga-zanga suka yi a birnin Rome na Italiya. Garin Venice na Italiya mai tsawon tarihi ya fuskanci ambaliya a kwanakin baya, inda magajin garin birnin ya daura alhakin abin da ya faru kan sauyin yanayi mafi tsauri cikin shekaru 50. An yi zanga-zanga a birane 138 na Italiya a cewar Fridays for Future da ke shirya zanga-zangar.
Sako ga gwamnati
'Yan gwagwarmya da yara 'yan makaranta a birnin Sydney sun shiga zanga-zangar neman matakai kan sauyin yanayi da ake yi a duk ranar Jumma'a inda suka je a helkwatar jam'iyyun da ke mulkin kasar ta Ostireliya. Masu zanga-zangar sun rike alluna da ke nuan cewa ana kassara rayuwar masu tasowa.
Dabbobi na fuskantar barazana
Masu zanga-zanga a Ostireliya sun nemi ganin an dauki matakan gaggawa kan wutar jeji da ta yi barna a makonnin da suka gabata. Wutar jejin da fari suna barazanar shafe wasu dabbobi daga doron kasa.
Japan — tsananin yanayi
Daruruwan mutane a birnin Tokyo na Japan sun yi zanga-zangar domin nuna goyon baya ga masu zanga-zanga duk Jumma'a. Japan tana cikin wuraren da ake ganin sauyin yanayi a shekarun da suka gabata. Kasar ta fuskanci ambaliyar ruwa mai dauke da iska mai karfi irin wannan ambaliya ta halaka mutane da dama a watan Oktoba cikin yankin arewa maso gabashin kasar.
Bunkasa jeji domin makoma ta gari
Masu zanga-zanga sun fito a kasar Indonesiya, a wani mataki na neman kare dazukan kasar. Gwamnati ta dakatar da noma kwakwan manja na wani lokaci. Masu gwagwarmaya suna nuku-nuku da yadda ake neman hana ganin gaskiyar yadda lamuran suke tafiya. An daura alhakin hada-hadar manja a duniya da yanjo kara tabarbara muhalli.
Fitar da iska mai gurbata muhalli
A Delhi birnin da ya fi gurbata a duniya, dalibai sun shirya maci zuwa ma'aikatar kula da muhalli suna neman ganin an kafa dokar ta baci kan sauyin yanayi. Kasar Indiya na sahun gaba wajen fitar da iska mai gurbata muhalli kuma tana dauke da birane 14 daga 15 da suka fi gurbata a cewar wani binciken Majalisar Dinkin Duniya.
Neman tattaunawa ta kasa da kasa
An yi zanga-zangar lokacin da kasashe 200 suke kulla yarjejeniyar neman kare muhalli a taron birnin Madrid na kasar Spain da ake kira COP25. Mahalarta taron za su share hanya yadda za a yi aiki da yarjejeniyar birnin Paris ta shekara ta 2025. Yarjejeniyar da ke neman zabtare iska mai gurbata muhalli.