1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Sudan na kara karfi

April 12, 2019

Kwararru a Sudan sun bayyana alkawarin da majalisar mulkin rikon kwarya ta sojin ta yi da cewa yaudara ce kawai. Sojojin dai sun ce ba za su kafe kan mulki ba.

https://p.dw.com/p/3Ghru
Sudan Demonstrationen
Hoto: picture-alliance/AA/O. Erdem

Kungiyar kwararru a Sudan, ta yi watsi da alkawarin da majalsar sojojin kasar suka dauka na cewar ba za su yi kememe kan mulki ba, bayan kifar da gwamnatin Shugaba Omar al Bashir da suka yi a jiya Alhamis.

Yayin wani gangamin da ya hada da kungiyar a yau Juma'a, kwararrun sun sa kafa sun shure ikirarin sojan na Sudan.

A yau ne dai shugaban rikon gwamnati Ahmed Awad Ibn Auf, ya nesanta abin da suka yi da yunkurin kwace iko, yana mai cewa sun yi hakan ne don bai wa matasan kasar damar tsara yadda za a sama wa Sudan wata gwamnati ta dimukuradiyya.

Kwararrun dai sun jaddada cewar za su ci gaba da zaburar da matasa da su bijire wa dokar ta-baci da ma ta hana zirga-zirga da sojojin suka kafa.