1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Sudan na kara tsanani

December 24, 2018

Kungiyar likitoci a Sudan, ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai illa masha Allahu, don nuna goyon bayansu ga masu zanga-zanga kan tashin farashin makamashin mai da kuma Burodi. 

https://p.dw.com/p/3AaBo
Sudan Khartum Anhänger  Sadiq al-Mahdi  Opposition
Hoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

A wannan Litinin ce a cewar likitocin na Sudan za su fara yajin aikin, koda yake sun ce suna iya duba masu bukata ta gaggawa.

Kungiyar ta kuma ce lallai ne su nuna fushin saboda karfin da jami'an tsaro suka yi amfani da shi kan jama'a.

An dai yi zargin jami'an tsaron na Sudan sun yi amfani da harsasan gaske kan masu zanga-zangar, inda akalla mutum tara ne aka tabbatar da mutuwarsu.

Zanga-zangar ta faro ne a makon jiya a wasu biranen gabashin Sudan din, tuni kuwa ta bazu zuwa wasu sassanta.