Facebook ya musanta yada labaran karya kan corona
July 17, 2021Talla
Shafin Facebook ya musanta zargin yada labaran karya kan cutar corona ne a matsayin martani kan kalamn da Shugaban Amirka Joe Biden yayi, inda ya zargi shafukan sada zumunta irinsu Facebook din, da yada baiyanan karya kan alluran riga-kafin corona a shafukan na su.
Furucin Biden ya biyo bayan samun karuwar alkaluma na masu kamuwa da cutar a makon da ya gabata a cikin kasar, inda ya ce annobar na sanadiyyar mutuwar jama'a da dama a sakamakon dogaro da jama'a ke yi, da baiyanan karya kan alluran rigakafin cutar da shafukan sada zumunta kamar Facebook din ke yadawa.
Amirka ta kasance daya daga cikin kasashen duniya da cutar corona ta yi wa illa sosai, kuma kawo yanzu kasar na fadi tashin ganin ta dakile cutar baki daya daga cikin kasar.