Zargin kisan mutane duk rana a Sudan ta Kudu
October 19, 2016Talla
Masu sanya idanu kan shirin zaman lafiya a Sudan ta Kudu sun bayyana cewa a kowace rana a na karya yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla abin da ka iya jawo babban tashin hankali da za a gaza shawo kansa a kasar.
Festus Mogae tsohon shugaban kasar Botswana da ke sanya idanu kan yarjejeniyar ya bayyana a ranar Laraban nan cewa a kowace rana ana karya yarjejeniyar daga dukkanin bangarorin hadi da aikata fyade ga mata da kisan fararen hula.
Jagoran aikin wanzar da zaman lafiya daga MDD Herve Ladsous ya fada wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a wannan mako cewa gwamnatin ta Sudan ta Kudu na ci gaba da yin kafar ungulu ga shirin kai dakarun wanzar da zaman lafiya 4,000 zuwa kasar.