1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Shugaba Kiir da hannu a rikicin Juba

Yusuf BalaSeptember 9, 2016

Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kazamin rikicin da ya barke a birnin Juba na Sudan ta Kudu a watan Yuli da ya sa Riek Machar ya tsallake manyan jami'ai a kasar na da masaniya a tada rikicin.

https://p.dw.com/p/1Jyoi
Südsudan Präsident Salva Kiir
Shugaba Salva KiirHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa kazamin rikicin da ya barke a birnin Juba na Sudan ta Kudu a watan Yuli da ya sanya mataimakin shugaban kasa kuma tsohon jagoran 'yan tawaye Riek Machar ya tsallake daga kasar manyan jami'ai a kasar na da masaniya a tada rikicin.

Wasu rahotanni na sirri da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu da nazarinsu a ranar Alhamis, sun nunar da cewa a tada rikicin na Juba a ranar takwas ga watan na Yuli ko ma bada umarni, akwai hannu na Shugaba Kiir da shugaban rundinar sojan kasar Paul Malong. Wasu rahotanni da a ke jiyo jami'an kasar na tattaunawa sun nunar da cewa babu wanda zai amfani da jirgin sama mai saukar ungulu cikin sojan kasar ba tare da masaniya ba ta Shugaba Kiir ko Malong.

Kwamitin dai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rikicin tsakanin ranakun takwas zuwa sha daya ga watan Yuli ya yi sanadi na rayukan mutane 300 baya ga dubbai da suka tsallake daga gidajensu,sannan an aikata fyade musamman daga 'yan kabilar Dinka da suka mamaye sojan kasar kan mata da yara 'yan kabilar Nuer .