1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigilar mutane 108 zuwa Libiya ba bisa ka'ida ba

Zainab Mohammed Abubakar
July 31, 2018

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD na nazarin yiwuwar take dokar kasa da kasa wajen jigilar wasu 'yan gudun hijira kimanin 108 zuwa Libiya bayan jami'an tsaron ruwa na Italiya sun cetosu daga teku.

https://p.dw.com/p/32O0K
Spanien -  Ankunft von Fluechtlingen in Andalusien
Hoto: picture alliance/CITYPRESS 24/f. Passolas

A martaninsa dangane da zargin ta dandalin sada zumunta na Facebook, ministan cikin gida Matteo Salvini ya ce, babu hannun jami'an tsaron ruwan Italiya a aikin ceton balle jigilar 'yan gudun hijirar,  jami'an kasar Libiya ne suka aiwatar da shi a ta gabar tekun da ke bangarensu.

Babban kwamisshionan MDD mai kula da 'yan gudun hijira a Italiya, ya sanar ta shafinsa na Twitter cewar, tashar jiragen ruwan Libiya ba wuri ne da ya cancanci 'yan gudun hijirar ba, wanda ya sa daukarsu zuwa tashar ya zama keta dokar kasa da kasa.

Wani dan majalisar Italiya Nicola Frantoianni, ya ce akwai shaidar da ke tabbatar da yadda jirgin ruwan Italiya mai suna Asso Ventotto ya yi jigilar 'yan gudun hijirar zuwa Libiya, wanda idan hakan da umurnin jami'an tsaron ruwan Italiya ne, ya sabawa dokar kasa da kasa.