1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Angola

Lawal, TijaniSeptember 23, 2008

Yadda jaridun Jamus suka bayyana zaɓen da aka yi a Angola

https://p.dw.com/p/FH6z
Wata mata na kaɗa ƙuri'a a AngolaHoto: picture-alliance/dpa

Babban dai abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon shi ne sakamakon zaben da aka gudanar a kasar Angola, wanda ko da yake jam'iyyar hamayya ta Unita ta amince da kayen da ta sha, amma ake zargin caba magudi a cikinsa. Amma da farko zamu duba rahoton da jaridar Financial Times Deutschland ta rubuta ne dangane da kwadayin da Jamus ke yi na samun gas daga tarayyar Nijeriya. Jaridar ta ce:

"A wannan makon sai da ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeir ya fito fili yayi gargadin cewar bai kamata kamfanonin kasar su zama 'yan rakiya ba a tsarereniyar zuba jari a nahiyar Afurka." Jaridar ta ce: Akalla a wannan bangaren Jamus na fafutukar shiga a dama da ita a fafutukar neman cin gajiyar albarkatun mai da gas da Allah Ya fuwace wa Nijeriya. To sai dai kuma a yayinda fadar mulki ta Berlin ke kokarin zayyana wani kawancen makamashi da kasar ta yammacin Afurka, tuni kamfanin Gazprom na Rasha, wanda kasashen Turai ke neman 'yantar da kansu daga gare shi, ya cimma yarjejeniyar hadin kai da kamfanin man Nijeriya NNPC. Ita dai Rasha so take ta kara kuntata wa kasashen Turai. Domin a baya ga Nijeriya kasar na ma'amalla da Libiya da Aljeriya, kuma tuni ta shiga tattaunawa da kasashen Ghana da Cote d'Ivoire da Namibiya."

Ita ma China ba a barta a baya ba a wannan tsarereniya, inda ba ta shayin ba da hadin kai ga kowace irin gwamnati ce a kokarinta na samun makamashi a nahiyar Afurka, in ji jaridar ta Financial Times Deutschland.

A zaben da aka gudanar a kasar Angola, jam'iyyar hamayya ta Unita ta amince da kayen da ta sha. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Sakamakon wannan zabe na majalisar dokoki na mai nuna alamu ne cewar jam'iyyar MPLA dake mulki ita ce zata lashe zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa shekara mai zuwa. Ba kuwa komai ne ya samarwa da jam'iyyar Unita koma baya ba illa kuskuren da tayi a zamanin baya inda ta koma yakin sunkuru bayan da tayi asarar zabe na demokradiyya a shekara ta 1992."


Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Angola dai kasa ce mai karfin tattalin arziki kuma tana da cikakken ikon samun ci gaba da yakar matsalar talauci tsakanin al'umarta. Muhimmin abin da kasar ke bukata shi ne kwararru, wadanda zasu taimaka mata ta kawar da tabon da yakin basasarta ya haifar da kuma sake gina kasar. Angola dai har yau tana samun tallafin raya kasa daga ketare. Amma fa muddin wannan tallafin na taimakawa ne shuagabannin kasar su rika arzuta kansu da kansu daga kudaden shiga da take samu daga cinikin mai to kuwa wajibi ne kasashen dake ba da wannan taimako su canza salon tunaninsu."