040908 Angola Parlamentswahl
September 5, 2008A yau ne masu kaɗa ƙuri´a a Angola su kimanin miliyan 8.5 ke zaɓen ´yan majalisar dokoki karo na biyu tun bayan shekarar 1992. Ko da yake hukumar zaɓe ta ba da tabbacin cewa za a yi zaɓen gaskiya da adalci wato saɓanin yadda ya kasance a ƙasashen Kenya da Zimbabwe ba, to amma masu sa ido a zaɓe sun nuna shakku ga wannan iƙirarin.
Yayin da jam´iyar MPLA mai jan ragamar mulkin ƙasar ta Angola tun bayan samun ´yancinta daga ƙasar Portugal shekaru 33 da suka wuce ta ƙara ƙarfi a lokaci guda kuma jam´iyar ta shugaban ƙasa mai cikakken iko Jose Eduardo dos Santos ba ta shirin raba iko da ´yan adawa da sauran ƙungiyoyin jama´a. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da aka yi amfani da wasu hanyoyi da ba su dace ba wurin yaƙin neman zaɓe.
Shugaba Jose Eduardo dos Santos a wani gangamin zaɓe a birnin Luanda inda ya ke cewa: "Abu ɗaya muke so wato ƙuri´ar ´yan Agola ga jam´yiar MPLA. Allah Ya ja zamin MPLA. Ana ci-gaba da gwargwarmaya kuma nasara ta na gare mu."
Ɗaiɗaikun jam´iyu 10 da kuma na kawance guda huɗu ke takarar zaɓen na shiga majalisar dokokin ƙasar ta Angola mai kujeru 320. Sannan a baɗi idan Allah Ya kaimu za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar. Bisa abubuwan da suka wakana a lokacin yaƙin neman zaɓen na ´yan majalisa ana iya hasashen yadda zaɓen shugaban ƙasar zai kasance a baɗi wato inda shugaba Dos Santos zai zama tamkar shi ne wuƙa shi ne nama. A halin da ake ciki shi ke iko da fagen siyasar ƙasar da kafofin yaɗa labaru, tattalin arziki da kuma batulmalin gwamnati. An kashewa jam´iyar maƙudan kuɗaɗe yayin da ´yan adawa suka tashi a tutar babu. Saboda haka magoya bayanta suka yi imanin lashe zaɓen na yau da gagarumin rinjaye, kamar yadda wani ɗan gani kashenin jam´iyar MPLA ya nunar.
Ya ce: "Yau rana ce mai muhimmanci a garemu. Muna jinjinawa shugaban MPLA. Tun yanzu mun sa cewa jam´iyar ta riga ta yi nasara. Jira muke yi kawai a kammala kaɗa ƙuri´a."
Babbar jam´iyar adawa ita ce tsohuwar ƙungiyar ´yan tawaye ta UNITA wadda tun a 1992 ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnati, to ama bayan zaɓe na wancan lokaci wani sabon yaƙin basasa ya sake ɓarkewa, sai bayan mutuwar shugabanta Jonas Savimbi a shekara ta 2002 zaman lafiya ya wanzu a Angola.
A lokacin yaƙin neman zaɓe magoya bayan shugaban kasa sun ta tursasawa ´yan adawa sannan an hana su damar yin kamfen ta kafofin yaɗa labarun hukuma. Saboda haka ne ma ´yan adawan da jami´an sa ido a zaɓe ke da ra´ayin cewa a cikin irin wannan yanayi ba za a yi adalci a zaɓen ba.
A halin da ake ciki cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a ƙasar yayin da giɓi tsakanin matalauta da masu arziki ke ƙaruwa. Hakan kuwa na faruwa duk da ɗinbim arzikin man fetir da kasar ke da shi.