1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Majalisar Dokoki a Kosovo

December 13, 2010

A yau Litinin, Hukumar zaɓe za ta bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen 'yan Majalisar Dokoki a Kosovo i

https://p.dw.com/p/QWjN
Frime Minista Hashim Thaci, da matarsa Lumnije.Hoto: picture-alliance/dpa

Jam´iyyar Frime Minista Hashim Thaci ta Democratic Party of Kosovo wato PDK ta yi iƙirarin lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar a jiya Lahadi, wanda ke zama na farko a ƙasar, tun da ta ɓalle daga ƙasar Sabiya a shekarar 2008. A na sa ran fitar da sakamakon ƙarshe a yau Litinin, amma sakamakon wucin gadin da aka fitar na nuna cewa Jam´iyyar Frime Minista Thaci ta fi samun rinjaye, wanda kuma a cewar Frime Ministan, manuniya ce ta goyan bayan al'ummar ƙasar ga manufofin sa. Jam´iyyar PDK, ta na neman ta sanya Kosovo a tafarkin da zai kai ta ga shiga ƙungiyar Tarayyar Turai, ko da ya ke ta na fama da cin hanci da rashawa, da ma rikicin ƙabilanci tsakanin kabilar Albaniya da ta tsageru na Sabiyawa.

Hukumar zaɓen dai ta tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin adalci ko da yake mutune ƙalilan suka fito suka kaɗa ƙuri'un su.

Mawallifiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi