1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargin jami'an tsaro da yi wa mata fyade a Zimbabuwe

Gazali Abdou Tasawa
January 31, 2019

Wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a a Zimbabuwe sun zargi jami'an tsaron kasar da yi wa mata fyade a kokarinsu na murkushe zanga-zangar da ta barke a kasar bayan da gwamnati ta kara kudin man fetur. 

https://p.dw.com/p/3CXGm
Polizisten in Harare, Simbabwe
Hoto: imago/Gallo Images

Kungiyoyin sun a lokacin kwantar da tarzomar matakan da jami'an tsaron kasar ta Zimbabuwe 'yan sanda da sojoji suka yi amfani da su ba su tsaya ba buda wuta kan masu zanga-zangar ko kuma kisansu da kulake, a a ta kai su ga tilasta wa mata masu yin lalata da su har a cikin gidajen iyalai da dama. 

Kungiyoyin kare hakkin jama'a da dama na kasar ta Zimbabuwe da suka hada da kungiyar Justice for Women's Rights Zimbabuwe sun ce sun samu koke-koken fyaden daga akalla mata 20. 

Kungiyoyin sun ce yanzu haka akwai tarin wasu matan wadanda jami'an tsaron suka yi wa faden a cikin gidajensu da amma suka kasa kai kara a bisa dalillai dabam-dabam. Sai dai a yanzu sannu a hankali wasunsu na tunkarar kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasar da matsalar.