Zimbabuwe ta kaddadamar da shirin yaki da cin hanci
December 15, 2019Hukumar yaki da cin hanci na cigaba da aikin bankado jami'an gwamnatin Zimbabuwe da suka azurta kan su da kudin kasar, cikin wani aikin farfado da tattalin arzikin kasar da shugaban kasar ya kaddamar.
Tun da farko hukumar ta gano yadda matar mataimakin shugaban kasar ta mallaki wani katafaren gida a rukunin gidajen masu hannu da shuni a kasar Afrika ta Kudu. Har yanzu mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga wanda ya jagoranci hambarar da gwamnatin shugaba Robert Mugabe ya tsuke bakinsa game da tuhumar da matar ta sa ke fuskanta. Kasar Zimbabuwe dai ta kara tsunduma matsalar tattalin arziki jim kadan bayan darewar shugaba Emmerson Mnangagwa karagar mulki duk kuwa da irin alkawurran da ya daukar wa al'ummar na inganta al'amura cikin kankanin lokaci.