1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Emmerson Mnangagwa ya lashe zabe

Yusuf Bala Nayaya
August 2, 2018

Mnangagwa ya samu kashi 50.8 na kuri'un yayin da babban abokin adawarsa Nelson Chamisa ya samu kashi 44.3 cikin dari. Chamisa ya ce ba makawa sai ya kalubalanci sakamakon.

https://p.dw.com/p/32VQj
Simbabwe Wahl | Emmerson Mnangagwa, Präsident
Hoto: picture-alliance/Photoshot/S. Jusa

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Litinin inda ya samu sama da kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben da ke zama na farko tun bayan kawar da gwamnatin Shugaba Robert Mugabe.


Mnangagwa ya samu kashi 50.8 na kuri'un yayin da babban abokin adawarsa  Nelson Chamisa ya samu kashi 44.3 cikin dari. Dan adawar dai ya bayyana cewa ba makawa sai ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotu ko a kan tituna.

Simbabwe Wahl | Sieg für Emmerson Mnangagwa, Präsident | feiernde Anhänger
Magoya bayan Mnangagwa na murnar yin nasaraHoto: Getty Images/D. Kitwood

Duk da cewa an yi zaben lami lafiya, barkewar rikici a ranar Laraba bisa zargin 'yan adawa cewa an tafka magudi a zaben, su kuwa sojoji suka mayar da martani da kisan mutane, hakan dai ya sanya an fara tuna lokacin tsohon Shugaba Mugabe da sojoji ke marawa baya a kasar.