Zimbabuwe: Kotu ta amince da matakin soji
November 25, 2017Kotun ta ce matakin da sojojin suka dauka na hanawa wasu na kusa da shugaba Mugabe amfani da karfin iko wajen hawa kan madafun iko bai sabawa dokokin kasar ba. Sai dai kuma kotun ta ce duk mutumin da ba'a zaba ba, ba zai iya gudanar da aikin da sai wanda aka zaba yake yi ba. Wannan bayani dai ya soma sanya shakku a wajen halascin shugabancin sabon shugaban na Zimbabvuwe Ermmerson Mnangagwa.
Wasu 'yan kasar ta Zimbabuwe ne dai guda biyu suka kai kara a kotun kolin kasar a cewar gidan talbijin din na ZBC. A cikin daren 14 zuwa 15 ga wannan watan na Nuwamba ne dai sojojin na Zimbabuwe suka kwace iko daga shugaba Robet Mugabe a wani mataki na nuna kin amincewarsu da korar mataimakin shugaban kasar Ermmerson Munangagwa wanda a halin yanzu ya zamo shugaban kasar. A ranar Juma'a ce dai aka rantsar Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar ta Zimbabuwe na riko, wanda ya sha alwashin nuna bambanci da mulkin Mugabe tare da bunkasa tattalin arzikin kasar.