Zimbabwe:Tankokin yaki a birnin Harare
November 14, 2017Wata mata da aka tattauna da ita cewa ta yi ta ga jerin motocin soja ciki kuwa har da tankokin yaki sun fice, sai dai ba ta san inda za su ba. Shi kuma wani da ya gane wa idanunsa lamarin, ya ce basu san dalillan fitowar ayyarin motocin na soja ba, domin abu ne da ba a saba gani ba.
Cikin wani kasheidi ne dai da ya yi a ranar Litinin 13 ga wannan wata na Nuwamba, babban hafsan hafsoshin kasar ta Zimbawe Janar Constantino Chiwenga, ya soki matakin korar mataimakin shugaban kasar ta Zimbabwe daga mukaminsa, inda ya sha alwashin cewa sojoji ba za su zura idanu suna kallo ba, idan har ba a dakatar da korar mutane daga cikin jam'iyya mai mulkin kasar tun daga shekara ta 1980 ta Zanu-PF ba.
Mataimakin shugaban kasar ta Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, mai shekaru 75 da haihuwa da aka jima ana yi wa kallon wanda zai gaji kujerar ta Shugaba Mugabe, an sauke shi daga mukaminsa a makon da ya gabata wanda tuni ya gudu ya bar kasar.