Zinare ya sauya komai
Bantako wani karamin kauye ne a kudu maso gabashin kasar Senegal. Lokacin da mutanen kauyen suka gano zinare a 2008, salon rayuwarsu ta sauya daga noma da aka san su da ita tun kaka da kakanni, zuwa fannoni daban-daban.
Gano albarkatun zinare a Senegal
"Lokacin da muka gano zinare a 2007-2008, kauyen ya sauya baki daya inji Doussa, jagoran cibiyar hakar ma'adanin zinare a kauyen Bantako. "A 2007 mutane 2000 ne a nan yanzu an haura 6000." Mutane kimanin 3000 ne ke aiki a mahakar ma'adanin Bantako a kowace rana, inda suke tono dutse mai dauke da burbushin zinare.
Rami na wucingadi
Yankin ma'adanin zinaren na karkashin mahukuntan kauyen, amma ba a hukumance ba, su na tabbatar da kowane ma'aikaci yana da katin shaida daga minista a Dakar. Sai dai katin bai wadatar ba. "Kamar yadda ake gani, babu jami'an jiha a nan, mu mutanen kauye ke kula da ma'adanin zinaren." a cewar Doussa. An haka daruruwan ramuka wato "Duma" a matsayin tushe.
Fitowa daga rami
"Na zo nan na yi aiki ne kawai a cewar Mamadou, dan kasar Guinea. "a kauyenmu, babu aiki. A nan ina ina tara kudi da zan tura gida, shi ne kadai abin da na damu da shi. "Ka'idojin aikin suna da tsauri. Babu kariyar lafiya da hakkokin ma'aikata. Mu ne koma baya na kasuwa mai riba inji Akia, shugaban rukunin ma'aikata da ya hada da mamadou.
Ruhin man fetur
Kafin bullar ma'adanin zinaren, babu Babura a kauyen. Harkar zinaren da bukatar ma'aikata na isa yankin mai muhimmanci cikin hanzari, Kedougou, na tazarar kilomita 35 daga Bantako. Masu sayar da man fetur da makanikai da sauran harkoki sun habaka a kauyen, tare da amfanar al'ummar da sauya rayuwarsu.
Tarin Fatanyu da garma
A kan babbar hanyar Bantako, daruruwan kananan shaguna da 'yan bukkoki na kwano suna sayar da kome da ma'aikatan hakar zinaren ke bukata. Malik ya ce ''na zo nan ne kawai na bude kasuwanci" asalinsa dai dan wani yanki ne a Senegal. Abin mamaki, yan shekaru da suka wuce babu wanda ya tsammaci wadannan harkoki a wannan kebabben kauye na Senegal.
Daga noma zuwa hakar ma'adinai
"Kafin samun zinaren da kyar ka ke ganin ginin bulo inji Waly Keita mai shekaru 45, wanda ya zama mai hakar ma'adanin zinare lokacin da aka gano ma'adanin mai daraja. " Hatta gida na wanda yanzu aka gina da bulon sumunti, ai da na cigaba da zama manomi da ba zan iya gina shi ba. Saboda haka ina gani kauyen ya amfana da wannan harka."
Salon fasahar hannu
Mahaka wadanda ba za su iya sayen na'urori masu nagarta da kuma ke da tsada ba, wanda ke fidda zinare daga cikin dutse, na amfani da masu sauki wajen aikin. Ana amfani da tsoffin injina wajen fasa dutsen, a jika a ruwa sannan a shanya, bayan ya bushe a sake fasawa.
Kowa da kowa
A duk sawon matakin fasa dutsen, akan fasa baguzan a karo na biyu, sannan a jika ya sha ruwa, kana a tace da fatan samun zinare da ya makale. Kusan dukkan iyalai na shiga a yi aikin da su, musamman a lokacin bazara, lokacin da makarantu ke hutu.
Babu wanda ke tunanin muhalli
Habakar tattalin arziki a kauyen da kuma kwararar dubban ma'aikata yana da nasa illar. Kasancewar babu wani tsarin zubar da shara ya haifar da tarin bola, kuma rafin da ya ratsa ta kauyen ya zama matattarar zuba shara. "Wata rana zinaren zai kare amma ina mamakin abin da zai faru da kauyen a lokacin kamar yadda Keita ya yi tunani.