1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban gwamnatin Jamus a Saudiyya

Usman Shehu Usman
September 23, 2022

Makasudin ziyarar kan manufofi ne na kare hakkin dan Adam a kasashen yankin Gulf, wanda ya sa ake samun matsala a dangantaka da wadannan kasashen. Amma ta fuskar manufofin makamashi, Jamus ta dogara da su

https://p.dw.com/p/4HHUt
Bildkombo | Olaf Scholz un Mohammed bin Salman
Hoto: Michael Kappeler/Bandar Aljaloud/AP Photo/dpa/picture alliance

A cikin watan Afrilun 2017 tsohuwar shugabar gwamnatin Jamjus Angela Merkel ta ce babu kokwanto kan samun cigaba wajen kare hakkin bil'adama a kasashen. Ta fadi hakan ne bayan wata ganawa da ta yi da Sarkin Saudiyya a Jeddah. Ga shugabar gwamnatin a bayyane take Saudi Arabia abokiyar tattalin arziki ce amma ta na da nakasu idan ana batun yancin dan Adam. 

Bayan shekaru biyar, magajinta Olaf Scholz na ziyara a kasar ta Saudi Arabiya duk da cewa ya saba wa tsarin siyasar da aka sauya a wasu lokuta a baya. Sebastian Sons, Masani ne kan harkokin Saudi Arabiya.

Saudi Arabien Scholz G20-Finanzministertreffen
Scholz a Saudiyya lokacin taron ministocin kudi na G20 Hoto: photothek/picture alliance

"Ya zuwa yanzu, Saudiyya ba ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da makamashi ba, kana da dangantakar Saudiyya da Jamus. Wannan na faruwa ne saboda ana ganin a fagen siyasa, Saudi Arabiya abokiyar zama ce mai matsala. A takaice dai huldar ta zama abokin da mutun baya son yin aiki tare da shi, hakan kuwa yana da alaka da yanayin 'yancin dan Adam, haka kuma yana da alaka da kisan Jamal Khashoggi da kuma shigar sojojin Saudiya a yakin Yemen“.

Idan an zo batun kare hakkin jama'a Jamusawa sun fi yin amanna da kasar Katar maimakon Saudiyya, ko da yake yanzu lamarin sannu a hankali yana sauyawa bisa bukatar makashi, kasashen yamma na ganin Yarima Bin Salman a matsayin abokin tafiya wanda ke son zamanartar da Saudiyya. Ko da yake manyan kawayen Saudiya kamar Amirka, sannu a hankali sun fara janyewa daga yankin na Gurlf inda suke maida hankali kan kasashen Asiya da ke kusa da China. A cewar Simon Engelkes, mai ba da shawara ga kasashen Gulf a gidauniyar Konrad- Adenauer.

“Tabbas alakar Saudiyya da Amirka ta dan yi kyau a karkashin mulkin Trump fiye da yadda take a yau. Har yanzu dai akwai baraka a alakar da ke tsakanin su, amma a bisa ka'ida kuma dangane da irin sukar da gwamnatocin biyu suka yi wa Saudiyya musamman ma yarima mai jiran gado. Domin ba shakka abubuwa da yawa suka haddasa hakan misali kisan Kashoggi da dai sauransu“.

Saudi Arabien | Öl-Lager am Hafen von Jubail
Matatar mai ta Jubail a kasar SaudiyyaHoto: Bilal Qablan/AFP/Getty Images

Saudiyya ta fahimci cewa, don aiwatar da tsare-tsarensu, da aka yiwa lakabi muradun 2030, na sake fasalin tsarin tattalin arzikinsu, kasar a mahangar tana bukatar abokan huldar kasashen yamma. Shugabannin siyasa ma sun san da haka kuma a bisa cimma wadannan muradun akwai wuraren tuntuba a tsakanin Saudiya da bangaren gwamnati Jamus. A ta bakin masanin siyasar Saudiyya.

“Don haka idan ka dubi kasar Saudiyya, mamba ce ta G20 kuma tana daya daga cikin kasashe goma masu karfin tattalin arziki a duniya a matsayin mai arzikin man fetur. Wannan yana nufin cewa kasa kamar Jamus, wacce ita ma tana da tsarin tattalin arziki mai karfi, kuma tana kallon duniya yadda tsarin sayar da kayayyaki zuwa kasashen waje ke sauyawa, ba za ta iya kallon yanayin tattalin arzikin duniya ba kawai don la'akari da manufofin tattalin arzikin Saudi Arabiya“

Masharhanta na cewa ita ma Jamus a nata bangaren, kamata ya yi ta guji yi wa masarautar kallon raini. Ana bukatar muhawarorin gaske kan alakar kasashen biyu. Sannan kuma za a iya daidaita manufofin siyasa na hakika da 'yancin dan Adam da kuma halin mutunta juna cikin tattaunawar wasu batutuwa da ake sabani a kansu,