Ƙarshen taron Senegal a game da cutar murra tsintsaye
February 23, 2006Talla
Nan gaba a yau ne, a Dakar babban ƙasar Senegal, za a kamalla zaman taro, tsakanin ƙurraru ta fannin kiwon lahiar dabbobi, da su hito daga ƙasashen yamacin Afrika da Mauritania, da kuma hukumomin kiwan lahia na Majalisar ɗinkin dunia, a game da cutar murra tsintsaye.
A tsawan yini 2, mahalarta wannan taro, da ƙungiyar Ecowas, kokuma CEDEAO, ta gayyata ,sun yi masanyar ra´ayoyi a game da matakan riga kafi ga cutar murra tsintsaye da ta ɓulla a Nigeria, wada kuma ke barazanar kutsawa a sauran ƙasashen maƙwabta.
Ministar kiwon ta ƙasar Senegal , Oumou Khairi Gueye Seye Seck ,ta gabatar da wani daftari wanda ya shinfi da hanyoyi magance yaduwar cutar a Afrika.
Wannan matakai sun hada da masanyar bayyamai, tsakanin kasashe, da kuma kafa cibiyar binciken a kan