Mata fiye da miliyan tara ne suka karbi rijistar zaben 2023 a Najeriya, sai dai ana zargin maza da rashin bai wa matan dama a fagen siyasar kasar. Shin yaya tasirin shugabancin mata? Mai yasa ba sa samun goyon bayan 'yan uwansu mata? Shin da gaske mata suna da rauni a fannin shugabanci ko suna da adalci fiye da maza?