Ƙungiyar IS ta harbe matasa biyu a IraƘi
November 21, 2014Mayakan Ƙungiyar IS da ke gagwarmaya da makamai sun bindige wasu matasa biyu har lahira a bainan jama'a, bisa zarginsu da suke yi da haɗa kai da abokan gabansu na Iraƙi wato jami'an tsaro. Shaidun suka ce a dandalin wata sananniyar kasuwa ta Zab a lardin Kirkouk ne wannan kashe-kashe suka afku.
Ita dai wannan ƙungiyar da ke da kaifin kishin addini ta yi ƙaurin suna wajen kashe-kashe a yanka jama'a kamar rago a yankunan da ke ƙarƙashin kulawarsu a Iraƙi da kuma Syriya. Kashe-kashen baya-bayannan dai sune na sojojin Syriya 18 da kuma wani dan amirka da take garkuwa da shi tun a shekara ta 2013. Tuni dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi ita IS da aikata laifin kisan kare dangi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita. Abdourahmane Hassane