1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Taliban ta ƙasar Pakistan

May 13, 2011

Ƙungiyar Taliban ta Pakistan ta ce ita ke da alhakin tagwayen harin ƙunar baƙin waken da aka kai kan cibiyar horon sojan ƙasar ranar juma'a. To ko wace ce ƙungiyar Taliban ta Pakistan?

https://p.dw.com/p/11FiK
Taliban ta Pakistan ta ce ita ke da alhakin tagwayen harin ranar juma'aHoto: DW

A sanarwa ta farkon da ta bayar a hukumance, bayan kisan Osama bin Laden a ranar biyu ga watan mayu, sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yi amfani da kalmar Taliban, daidai yadda aka saba ji daga jami'an siyasar ƙasashen yammaci, tamkar dai wata tsayayyar ƙungiya ce mai shikashikan ɗaya:

US-Außenministerin Hillary Clinton
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton a jawanta na farko bayan kisan Bin Laden biyu ga watan mayuHoto: AP

"Har yau babu wani canji dangane da saƙonmu ga Taliban. Amma wataƙila a yau zasu ankara da hakan. Ba zaku iya ɓuya daga gare mu ba. Ba zaku iya samun galaba akanmu ba. Zaɓi ya saura gareku domin ku janye jiki daga Alƙa'ida ku shiga tattaunawar sulhu a siyasance."

Amma shin wace ƙungiyar ta Taliban Hillary Clinton ke nufi? Shin tana nufin Taliban ta Afghanistan ce dake ƙarƙashin Mullah Omar dake da dangantaka ta ƙut-da-ƙut da ƙungiyoyi irinsu Haqqani ko Hizbal-Islam ta Gulbuddin Hekmatyar? Ko kuwa dai ita Taliban ta Pakistan wata ƙungiya ce dake cin gashin kanta? Ɗan jaridar Pakistan Rahimullah Yusufzai, wanda ya gudanar da hira sau biyu da Osama bin Laden a shekara ta 1998, ya bayyanar a fili cewar akwai wasu ƙasashe biyu da Taliban ke yaƙi a cikinsu:

"Ita ma Pakistan tana fama da yaƙi yanzu haka. Ana fama da hare-haren ƙunar baƙin wake da farmakin Amirka ba tare da gargaɗi ba. Dukkan sojoji da 'yan sare ka noƙe sai kai wa juna hari suke. A taƙaice yaƙin ana gwabza shi ne a Afghanistan da Pakistan baki ɗaya."

Ba shakka yaƙin an gabatar da shi ne akan Alƙa'ida da Taliban, amma kuma yaƙin bai shafi ɗaya-ɗayan Taliban ba. Domin kuwa ƙungiyar Taliban ta farko ta samu ne bayan janyewar sojojin mamaye na Tarayyar Soviet daga Afghanistan a sansanonin 'yan gudun hijirar ƙasar a Pakistan kuma ƙungiyar ta samu goyan baya daga Pakistan da Saudiyya. Tun abin da ya kama daga 1996 zuwa harin ta'addancin 11 ga watan satumban shekara ta 2001 ƙungiyar Taliban ta Afghanistan ke da ikon akasarin yankunan ƙasar. Kuma tun daga 11 ga watan na satumban shekara ta 2001 ƙungiyar Taliban dake ɓangaren Pakistan ta fara samun ikon cin gashin kanta kamar yadda Ahmed Raschid masanin kimiyyar siyasa a ƙasar Pakistan ya nunar:

"Hakan ma dai ita ce ainihin dalilin da ya sanya ƙungiyar Taliban ta Afghanistan da Alƙa'ida suka samu kafar tserewa zuwa Pakistan. Sojojin Amirka da ƙawayenta ba su samu ikon murƙushesu ba. Sun samu mafaka a yankunan ƙabilun Pakistan suka samu kafar cusa zazzafar aƙida a zukatan jama'a kuma Alƙa'ida ta kashe maƙudan kuɗi akan wannan manufa."

Dossier 3 Pakistan Anschlag Peschawar
Sojojin Pakistan na cikin hali na tsaka mai wuyaHoto: AP

A yanzun dai sojojin Pakistan, waɗanda su ne ke jan akalar manufofin ƙetare da na tsaro na ƙasar na cikin wani hali na tsaka mai wuya. Domin kuwa a ɓangare guda suna fafutukar murƙushe ƙungiyar Taliban ta ƙasar, a yayinda a ɗaya ɓangaren suke sara tare da duban bakin gatari saboda ba su sha'awar asarar ƙungiyar Taliban ta Afghanistan a matsayin ƙawarsu wajen adawa da Indiya. Bugu da ƙari kuma ƙasar ta Pakistan tana da muhimmancin gaske ga Alƙa'ida tun bayan da ƙungiyar ta ankara da gaskiyar cewa matasa a ƙasashen Larabawa ba su buƙatar ta a fafutukarsu ta neman sauyi.

Mawallafi: Sandra Petersmann/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu