Ɓaraka tsakanin Amirka da Isra'ila
March 13, 2010Talla
Alamun ɓaraka tsakanin Amirka da Isra'ila sai ƙara
fitowa a fili suke yi. Sakatariyar harkokin wajen Amirka
Hillary Clinton ta ce sanarwar gina sabbin mutsugunan
Yahudawa 1,600 a gabashin birnin Ƙudus da Isra'ila ta
mamaye, wanda aka yi dai lokacin da mataimakin
shugaban ƙasar Amirka Joe Biden yake yankin, wani
cin fiska ne ga Amirka a faɗar Clinton. Sakatariyar
harkokin wajen Amirka wadda ta ɗauki mintuna 43
tana caccakar matakin da firayim ministan Isra'ila
Benjamen Netanyahu ya ɗauka, ba da safai akan ji
irinsa daga bakin wani jami'in gwamnatin Amirka ba.
Su ma dai Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai da ƙasar Rasha duk
sun yi Allah wadai da wannan matakin, wanda suka ce
taƙala ne, kana kuma wani babban tarnaƙi ne ga zaman
lafiya.
Mawallafi: Shehu Usman
Edita Mohammad Nasiru Awal