Ɓarin wuta tsakanin dakarun NATO da yan Taliban a Afghanistan
August 21, 2007Fiye da mutane 20 su ka rasa rayuka a sabuwar bata kashin da ta haɗa dakarun rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanistan da mayaƙan Taliban.
A cewar wata majiyar rundunar yan sandar Afghanistan, wanda su ka mutun sun haɗa da yan taliban19 da kuma jami´an tsaro 2.
Rikici mafi muni ya faru a yankin Ghazni, inda yan taliban ke ci gaba da yin garkuwa da mutunanen Korea ta Kudu 19, da kuma bajamishe ɗaya.
A cen ma yankin Helmand a na ci gaba da gwabza faɗa tsakanin ɓangarorin 2.
Tun makon da ya gabata ne, rundunar ƙungiyar tsaro ta NATO ta ƙaddamar da wani gagaramin hari, da zumar murƙushe yan taliban a wannan yankuna , to saidai ya zuwa yanzu, su na fuskantar turjiya ta ban mamaki daga dakarun Taliban.
A cewar Egon Bahr, babban jami´i ,mai kulla da hulɗoɗi da ƙasashen ƙetare na jam´iyar SPD a nan Jamus, samar da kwanciyar hankali mai ɗorewa a ƙasar Afghanistan na buƙatar ƙarin sojojin ƙasa da ƙasa masu yawa.