Shigar da mata cikin harkokin gudanarwa a arewacin Najeriya
November 12, 2018Talla
Batun sanya mata cikin harkokin gudanarwa da samar da zaman lafiya batu ne da ba safai wasu kasashe masu tasowa ke baiwa kulawar da ta dace ba. Wannan shi ya sanya Majalisar Dinkin Duniya karkashin shirinta mai "Lura da Mata na Duniya" wato UN-Women ta bullo da wani shiri na musamman a jihohi uku a arewacin Najeriya wanda aka yi wa taken “Tallafawa harkokin sanya Mata samar da zaman lafiya a arewacin Najeriya.