Adadin mutane da Isra'ila ta kashe a Gaza ya dara dubu 45
December 26, 2024Rahotanni dake fitowa daga Gaza sun bayyana adadin mutane da Isra'ila ta halaka a yakin da ta ke yi da Hamas ya kai 45,399.
Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce a cikin sa'o'i 24 kadai Isra'ilar ta yi ruwan wuta kan mutum 38 a yankuna daban-daban na zirin Gaza.
Isra'ila ta kashe akalla mutum 22 a zirin Gaza
Har ila yau, hukumomin lafiyar sun ce adadin mutane da suka samu raunuka ciki har da yara da mata ya kai 107,940 a cikin watanni 14 da fara yakin wato tun bakwai ga watan Oktoban 2023 kenan.
Wata kafar talabijin a zirin ta bada rahoton kashe mata 'yan jarida biyar a wani hari da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza.
Tattaunar Qatar ta gaza cimma daidaiton tsayar da yakin Gaza
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin duniya daban-daban sun yi ta kiran a tsagaita wuta da kuma dakatar da yakin Gaza amma kiran nasu bai sauya komai ba.