Tattaunar Qatar ta gaza cimma daidaiton tsayar da yakin Gaza
December 25, 2024Tirjiyar da kungiyar Hamas ta yi wajen kin bayar da sunayen Isra'ilawan da ta yi garkuwa a ranar 7 ga watan Oktoban bara ta janyo tsaiko ga tattaunawar samar da masalahar kawo karshen yakin Gaza, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka rawaito a Larabar nan.
Karin bayani:Paparoma ya yi kiran zaman lafiya da taimakon jinkai
Hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon sama da mako guda ana tattaunawa bisa jagorancin kasar Qatar, tsakanin Masar da Amurka da kuma Isra'ila, domin lalubo hanyoyi dakatar da yakin baki-daya.
Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa za su ci gaba da tuntubar juna a cikin gida kan yiwuwar ci gaba da tattaunawar sulhun da suke yi yanzu haka.
Karin bayani:Isra'ila ta aikata 'kisan kare dangi' a Gaza - Amnesty International
Rahotanni sun nuna cewa Hamas ta amince da shirin musayar fursunonin har ma ta fitar rukunin farko da za ta saki idan har aka cimma yarjejeniya, sai dai ta ki bayar da sunayen dukkan mutanen da ke raye yanzu a hannunta lokaci guda, kamar yadda isra'ila ta nemi sani.