1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karfafa alakar kasuwanci da Jamus

December 11, 2024

A ci gaba da kokarin habbaka ciniki, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya jagoranci wata tawagar 'yan kasuwa zuwa ziyarar aiki ta kwanaki uku a Najeriya.

https://p.dw.com/p/4o1t6
Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Ziyara | Frank-Walter Steinmeier | Jamus | Alaka
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da na Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Ubale Musa/DW

A tsakanin shekara ta 2017 zuwa shekaru biyu baya dai, ciniki a tsakanin Tarayyar Najeriya da 'yar uwarta Jamus ya tashi daga dalar Amurka miliyan dubu daya da 700 ya zuwa miliyan dubu biyu da 300. Adadin kuma da ke shirin da ya karu, tare da wata ziyarar shugaban Tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya zuwa Najeriyar a halin yanzu. Steinmeier da ke jagorantar wata tawaga ta masu kasuwar dai, zai share tsawon kwanaki uku kuma yana shirin karade biranen Abuja da Legas. Muhimman batutuwan makamashin wutar lantarki da na iskar gas ne dai, suka dauki hankalin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma babban bakon da ke ziyarar a Abuja. Kuma Shugaba Tinubun bai boye ba, wajen nuna godiyar Najeriyar a kan rawar da Jamus din ke takawa wajen daidaita hasken wutar lantarki a kasar.

Yadda Najeriyya ta ci moriyar hulda da kasar Jamus

Najeriyar dai na zaman kasa ta biyu a Kudu da Sahara cikin batun ciniki da Jamus, kuma ziyarar da ta kalli kamfanonin makamashi da daman gaske a fadar shugaban na Jamus ka iya sauya da dama a dangantakar da ke da tsohon tarihi. Wani shiri na habakar hasken wutar lantarki a tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Siemens na kasar Jamus da kuma ke da burin kara yawan wutar da megawatt kusan dubu 25 cikin wasu shekaru shidan da ke tafe dai, ya yi nisa yanzu haka. Kuma tuni Abujar a tunanin ministan wutar kasar Adebayo Adelabu ta fara ganin haske, cikin duhun rashin hasken wutar lantarkin Najeriyar. Daidaito cikin batun wutar ne dai ake wa kallon zakaran gwajin dafi ga Tarayyar Najeriya da ke tunanin girma, amma kuma ke kallon kalubale cikin makamashin mai tasiri.