Mahajjata da dama sun rasu a jifan shedan
September 24, 2015Mahukunta a Saudia sun ce , maniyata sama da 700 ne suka rigamu gidan gaskiya, sakamakon turmitsitsin da aka samu a kan hanyarsu ta zuwa jifan shedan a Mina.
‘Yan kwana-kwana dai na ci gaba da kwashe gawarwaki da wadanda suka jikkata,a yayin da jami’an tsaro ke kokarin sauya akalar maniyatan subi wasu hanyoyin don samun daidadituwar lamura .
Ba a dai kai ga gama tantance wadanne kasashe abin yafi ritsawa dasu ba, amma dai ma’aikatar lafiya ta ce yawancinsu tsofaffi ne.
Wata tsohuwa dake ci gaba da karbar magani a sibiti ta bayyana yadda abin ya faru;
Matsatsi ne sababi
“Muna kan hanyarmu ta zuwa Safa da Marwa, matsatsi ya yi matsatsi,sai kawai na ji nunfashina ya dauke.Daga nan ban san abin da ya faru ba. Na dai gammu haka zube a kasa jina jina.”
Wani da ke kusa da inda hatsarin ya faru ya dora laifin hatsarin kan hukumar shirya aikin hajjin Saudiya da kuma wasu kamfanonin lura da maniyyata.
Askarawa sun taka rawa
“A ganina dalilai biyu ne suka jawo wannan hatsari, na farko kuskuren da hukumar shirya aikin Hajji ta yi, na mayar da hanyar tafiya kadai ta zama ta zuwa da dawowa, kana askarawa sukai ta tura mutane wai don su wuce. Sai kuma rashin bin ka‘ida da kamfanonin lura da maniyata, yadda suke saba lokuta da hanyoyin da aka tsara zasu dinga bi.”
To sai dai ministan lafiyar kasar ta Saudiyya ya musunta gazawar hukumar aikin hajji da jami‘an tsaro, yana mai dora alhakin faruwar hatsarin kan rashin bin ka‘idar maniyata.
A farkon aikin Hajjin na bana dai, wanda mutane sama da miliyan biyu ke halarta, an fuskanci wani mummunan hatsari a lokacin da wata rumfa ta fada kan maniyata, wacce ta kai ga halakar fiye da mutane dari. Hatsarin da ya kai ga dakatar da kamfanin Bin Ladan da ya jima yana tarbar mahajjata, kana aka dakatar da jami‘ansa don gudanar da bincike.
A shekarun baya dai, an sha fuskantar turmutsitsi a wajen jifan shaidan din, amma bayan wasu gyare-gyare da mahukuntan na Saudiyya suka yi, an samu sauki a ‘yan shekarun nan.