1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harkokin mulkin Siriya na farfadowa

Suleiman Babayo AH
December 9, 2024

Harkokin rayuwa sun fara farfadowa bayan 'yan tawayen da suka mamaye Siriya sun fara tattauna kafa gwamnatin wucin gadi, inda firaminista ya ci gaba da rike madafun iko.

https://p.dw.com/p/4nvX1
Birnin Damaskus na kasar Siriya
Birnin Damaskus na kasar SiriyaHoto: Bekir Kasim/Anadolu/picture alliance

A wannan Litinin Fiministan kasar Siriya gami da majalisar ministocinsa sun ci gaba da gudanar da ayyuka daga ofisoshin gwamnati a birnin Damuscus, bayan mayakan 'yan tawaye sun kawar da Shugaba Bashar al-Assad wanda ya fice daga kasar. Firaminista Mohammed Ghazi Jalali zai ci gaba da jagorancin gwamnatin zuwa lokacin da za a kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar, kuma ya yi alkawarin ganin harkokin gwamnati sun ci gaba, yayin da 'yan Siriya da ke gudun hijira a kasashen ketere ke neman hanyar komawa gida.

Karin Bayani: Bashar al-Assad na Siriya ya samu mafaka a Rasha

Tuni harkokin rayuwa suka fara komawa sannu a hankali bayan Shugaba Assad ya tsere daga kasar ta Siriya, inda ake kyautata zaton yana kasar Rasha inda ya smau mafakar siyasa. Akwai dai wasu tsaffin manyan jami'an gwamnatin ta Assad da suka tsere. Sannan Firaminista  Mohammed Ghazi Jalali ya ce suna aikin kafa gwamnatin rikon-kwaryar cikin tsanaki.

Ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci samun zaman lafiya na siyasa da kafa gwamnatin da za ta magance matsalolin 'yan kasar gami da sake gina kasar ta Siriya bayan yaki.