Bashar al-Assad na Siriya ya samu mafaka a Rasha
December 8, 2024Rasha ta ba hambararren shugaban kasar Siriya, Bashar al-Assad tare da iyalansa mafaka ne bisa dalilan jin kai ne, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta TASS ta ruwaito. Rashar ta ce ta kira taron kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin domin tattaunawa a kan halin da ake ciki a Siriya, bayan da'yan tawayen HTS sun kifar da gwamnatin al-Assad.
Karin bayani: 'Yan tawaye sun karbe kasar Syria inda shugaba Assad ya arce
A gefe guda, Shugaban Amurka Joe Biden zai gana da masu ba shi shawara kan harkokin da suka shafi tsaro dangane da halin da ake ciki a Siriya. Amurka dai na da kimanin dakaru 900 a kasar ta Siriya da kuma wasu 2,500 a Iraqi, wadanda suke daga cikin kawance soji na kasa da kasa da aka samar a shekarar 2014 domin kakkabe 'yan ta'adda.