An kira sabon zabe a Isra'ila bayan gaza kafa gwamnati
May 30, 2019Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya fuskanci kalubale wajen kulla kawancen da zai ba shi damar kafa sabuwar gwamnati, lamarin da ya shi kira da a gudanar da sabon zaben 'yan majalisa watanni kalilan bayan gudanar da makamanci wannan zabe da jam'iyyarsa ta lashe.
Yini guda 'yan majalisar dokokin Isra'ila suka shafe suna muhawara tsakaninsu kan sharudan da jam'iyun adawa suka shunfuda kafin su shiga sabuwar gwamnatin Netanyahu. Amma kuma wannan bai hana wakin hula ya kai su ga dare ba, domin 'yan Likud da ke mulki sun tashi ba tare da samun goyon bayan da suke bukata wajen kafa sabuwar gwamnati ba. Lamarin da ya kai majalisar Isra'ila ta Knesset fasawa don kowa ya rasa ta hanyar kada kuri'ar rusa kanta da kanta, wata guda kacal bayan rantsuwar kama aiki biyo bayan zaben 'yan majalisar dokokina 9 ga Afirilu. Wannan ya na nufin cewa 'yan Isra'ila za su sake kada kuri'a a ranar 17 ga watan Satumba a karo na biyu cikin watanni biyar.
Benjamin Netanyahu mai shekaru 69 da haihuwa bai yi nasarar kafa kawance da jam'iyyun da ke da ra'ayin rikau da masu tsananin kishin addini Yahudu cikin lokacin da doka ta kayyade ba. sai dai maimakon barin shugaban kasar Reuven Rivlin bai wa shugaban wata jam'iyyar damar kulla kawancen kafa gwamnati, Firaministan ya zabi shirya sabon zabe, lamarin da ya sa ake zarginsa da neman dawwama a kan kujerar mulki don gudan tuhuma daga kotu. Sai dai Netanyahu ya dora alhakin tashi dutse hannun riga a kan Avigdor Libermann.
Babban abin da ke hana ruwa guda shi ne rashin jituwa da ake fuskanta kan batun horon aikin soja ga matasa tsaksanin 'yan Orthodox da 'yan jam'iyyar kishin kasa. Shugaban jam'iyyar Beiteinou Avigdor Lieberman ya nace kai da fata sai an amince duk matasa sun gudanar da horon aikin soja ba tare da la'akari da addininsu ba, lamarin da masu kare addinin Yahudu suka ce ba za ta sabu ba. Dama doka ta yafe wa 'yayansu yin wannan horo na soja. Mista Lieberman ya zargin jam'iyyar Likud ta Netanyahu ne ummal aba'isa sabon rikicin siyasa da Isra'ila ta samu kanta a ciki.
Wannan dai gagarumar koma baya ga mai Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya kwashe shekaru 10 yana jan zarensa a fagen mulkin Isra'ila ba tare da ya tsinke masa ba, inda ya shafe shekaru goma na baya-bayan nan a matsayin shugaban gwamnatin kasar. Sai dai shirya sabon zaben ya zame wa Firaministan na Isra'ila hanya mafi a'ala na ceto kansa daga rauni da yake fama da shi sakamkon zarge-zarge da ake masa ba cin hanci da rashawa.