1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zaɓi sabbin kwamishinoni na majalisar tarayyar Turai

Yusuf BalaOctober 22, 2014

Majalisar dokokin Kungiyar tarayyar Turai EU ta amince da sabbin kwamishinoni ƙarƙashin jagorancin sabon shugaba me shirin hawa karagar mulki, Jean Claude Juncker a ranar 22-10-14.

https://p.dw.com/p/1DZrJ
Juncker im Europaparlament 22.10.2014
Hoto: Reuters/Christian Hartmann

Mambobin majalisar ta Kungiyar EU a zaman taronsu na Strasbourg kashi 423 sun amince da sabuwar hukumar,yayin da mambobi 209 suka nuna ƙin amincewa,kashi 67 kuma ba su bayyana ba yayin kaɗa ƙuri'ar da za ta buɗe sabon tsarin da shugaba Juncker zai fara tafiya da shi a cikin wa'adin mulkinsa na shekaru biyar da zai fara a ranar daya ga watan Nuwamba.

Shirin kasafin kuɗi da majalisar ta tsara a shekara mai zuwa

A jawabinsa kafin buɗe kaɗa ƙuri'ar Juncker ya ce zai gabatar da shirin kashe maƙudan kuɗaɗe na Euro miliyan dubu 300 cikin shirin zuba jari da zai taimaka wajen samar da aiyyukan yi, da ci gaban tattalin arziki, a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun fargaba na tsoron sake komawar ƙasashen na Turai cikin rikicin tattalin arziki.

Treffen der EU-Finanzminister
'yan majalisar na tarayyar TuraiHoto: Picture alliance/dpa

Amma a cewar mashawarci na kusa ga sabon shugaban kuma lauya, Martin Selmayr shirin da ke gaban sabon shugaban ya fi gaban zuba kuɗi kawai.

''Wannan shirin zuba jarin kuɗi na Euro miliyan dubu ɗari uku da mista Juncker ya bayyana, ba shi ne mafita ba daga matsalar da ake fiskanta yanzu haka ba, muna buƙatar wani abu da zai samar da makoma mai kyau a tasakanin ƙasashen nan gaba, ba kawai sake inganta harkokin ba da basuka ba da mu ke da su a Kungiyar ta Tarayyar Turai.

Wannan hukuma dai ana kallonta a matsayin mafi ƙarfin cibiya da ke a Brussels, wacce ke tsara dokoki, da tsarin kasafin kuɗin ƙasashe, kuma ita ke da alhakin shiga tsakani kan batun harkokin kasuwancin ƙasashe da ƙasashen na EU. Halin da wasu ƙasashen na ƙungiyar suka sami kansu halin yanzu, na zama babban ƙalubale a gaban sabbin mahukuntan wannan ƙungiya.

Sabon shugaban ƙungiyar na da jan aiki a gabansa

A cewarsa sabon shugaban da ke jiran karbar aiki daga Jose Manuel Barroso da zai kammala shekarunsa goma na jagorantar hukumar ta EU, ya ce suna da manya-manyan ƙalubale a gabansu kamar yadda ya ke ƙarin bayyani.

Jean-Claude Juncker EU-Kommissionspräsident 09/2014
Jean-Claude JunckerHoto: Imago

''Da fari, a sabuwar Hukumar ta Kungiyar tarayyar Turai, muna da damarmaki da dama,dole mu yi ƙoƙari wajen shawo kan matsalolin siyasa a wasu yankunan, da kuma tallafa wa wajen farfaɗo da tattalain arzikin wasu ƙasashen. Muna buƙatar samar da dunƙulalliyar nahiyar Turai mu samar da ci gaban ƙasashen a samar da aiyyukan yi ga al'umma, ina ganin, ina da tawaga da ta dace mu aiwatar da wannan aiki.

Wannan hukuma dai, na da mamba ɗaya daga cikin ƙasashe 28 na Kungiyar ta EU, ƙungiyar da ke jan ragamar sama da mutane miliyan ɗari biyar na yankin da ke zama mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya. A cewar Mista Juncker Ƙungiyar ta EU dole ta ƙara azama.