Bikin Sallah cikin matsin arziki da tsaro a Najeriya
July 9, 2022A Najeriya a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bikin babbar Sallah, matakin da hukumar kula da birnin Abuja ta dauka na sanya dokar dole a rufe daukacin wuraren shakatawa na birnin da karfe 7 na maraice ya rage karkashin bikin a lokacin da al‘umma ke fama da matsaloli na koma bayan tattalin arziki da fargaba ta rashin tsaro.
Birnin Abuja hedikwatar Najeriya na cikin yanayi na bikin babbar Sallah da za a yi a ranar Asabar, inda mutane ke ta kai da komo na shirin wannan biki wanda duk da na musulmai ne amma sauran mabiya addinai ma ke cike da alwashi na hutawa musamman amfani da kyawawan wuraren shakatawa da ake da su a birnin, wadanda wasu kan wo takakka domin amfani da su a irin wannan lokaci.
Sai dai matakin da hukumar birnin Abujan ta dauka na sanya dole daga karfe bakwai na maraice a rufe wuraren ya dushen hanzarinsu.
An samu korafe-korafe daga mazaunan birnin a kan abin da wannan zai haifar musamman katse hanzarin samun kudadden shiga.
Amma hukumar kula da birnin Abuja ta mai da martani a kan abin da ya sa ta dauki wannan mataki da ma korafe-korafe da jama'a ke yi. Daukar mataki na bai daya a kan wuraren shakatawa na Abujan da kwararru ke ganin akwai gyara a ciki.
Hali na tabarbarewar tsaro a Najeriyar dai ya sanya daukan matakai mabambanta daga hukumar kula da birnin, kama daga rushe bukkokin da akan yi a filayen da ba a gina ba wadanda aka yi ba da izini ba, domin wurare ne da bata gari ke zama.
A bana dai alummar Abujan Eid el Kabir ko babbar Sallah ta zo masu a hali na koma bayan tattalin arziki da rashin tsaro, musamman bayan kai hare-hare a makwabtan birnin.