Birnin Kudus ta zama babban birnin Isra'ila
December 7, 2017Talla
Kasashen Turkiyya da Indunisiya na a cikin manyan kasashe da akafi samun yawan musulmai, sun kuma soki matakin da ce wa Amirkar ta saba tsarin Majalisar Dinkin Duniya na tun shekarun 1980 na na sauya birnin kudus a matsayin fadar mulkin Isra'ila.
Tun bayan bayyana sauya birnin na Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'aila, Falasdinawa ke zanga-zangar adawa da kudurin na Amirka.