Blinken na ziyara a Koriya ta Kudu
January 5, 2025Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya isa Koriya ta Kudu, a yayin da rikicin siyasar kasar ke ci gaba da rincabewa.
Mista Blinken ya je kasar da ta kasance kawar Amurka ne, bayan tsigaggen shugabanta ya ayyana dokar soja mai cike da cece-kuce a watan Disambar 2024.
An gaza kama shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige
Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da ke tare da sakataren ya ce, Blinken ya tsara tsayawa a kasashen Faransa da kuma Japan a yayin ziyarar
Wannan balaguron ka iya kasancewa na karshe ga sakataren harkokin wajen na Amurka, ganin cewa an kusa rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaba.
Koriya ta Kudu ta tsige sabon shugaban kasar
Amurka tana da karfin fada a ji a al'amuran Koriya ta Kudu saboda tallafin makamai da jiragen yaki da kuma kyakkyawar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.