Boko Haram: Yara 'yan gudun hijira na cikin wani hali
September 18, 2015A wani rahoto da ta fidda a Juma'ar nan (18.09.15), hukumar kula da kananan yara UNICEF ta ce irin ta'adin da rikicin kungiyar Boko Haram ya yi a Nijeriya da wasu kasashen da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru lamari ne mai munin gaske duba da irin yadda balahirar ta tilastawa kananan yara da mata masu tarin yawa barin muhallansu tare da lalata dukiyoyi masu yawan gaske.
A cikin rahoton da UNICEF din ta fidda, ta ce yara miliyan daya da dubu dari hudu ne aka hakikance cewar rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu kuma yanzu haka suna gudun hijira a wurare daban-daban. Rahoton ya cigaba da cewa a yankin arewacin Najeriya kadai kimanin kanan yara miliyan daya da dubu dari ne wannan batu ya shafa
Masana hallayar dan Adam irinsu da ke bada tallafi a guda daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira a Najeriya wanda ke kunshe da yara masu yawa sun ce halin da yaran ke ciki na da sosa rai don kuwa suna cikin damuwa matuka sannan yanayin lafiyarsu abar dubawa ce domin da dama na bukatar tallafi na kiwon lafiya.
A farkon shekarar nan dai hukumar ta UNICEF ta ce yi wa kananan yaran allurar rigakafi kamuwa da cuttuukan nan guda shidda masu hallaka kananan yara sama da dubu dari uku da sha biyar kana sama da dubu dari biyu kuma ta samar musu da ruwan sha mai kyau yayin da wasu da dama suka amfana da ilimi kamar yadda wani jami'in hukumar bada agaji ta Red Cross a jihar Bornon Najariya Mahmud Abubakar ya shaidawa DW.