Cece-kuce kan haramta zanga-zanga a Abuja
July 18, 2019'Yan sanda sun toshe masu zanga-zangar da suka fita domin yin gangami a wuri guda a birnin Abuja kasa da sa'o’i 24 bayan da sifeto janar na rundunar ‘yan sanda ya fitar da sabuwar ka'ida da ta haramta zanga-zanga a kan tituna kowace iri ce. Sai dai tuni kungiyoyi kare hakkin jama’a sun nuna rashin amincewa da ma dacewar wannan haramci daga ‘yan sandan.
Kakakin rundunar 'yan sanda Franka Mba ta bayyana cewa irin yadda masu zanga-zanga ke kawo cikas da ma lalata dukiyar jama’a ya sanya su daukan wannan mataki, domin a makonin nan an yi ta artabu da ‘yan Shi’a a birnin. Sai dai ra’ayoyi sun sha bamban a tsakanin ‘yan Najeriya a kan wannan batu, sanin cewa zanga-zanga na zama makami da talaka ke amfani da shi wajen nuna korafinsa a tsari na dimukuradiyya.
A yayin da wasu kungiyoyi ke shirin kalubalantar lamarin a gaban kotu, masharhanta na bayyana bukatar sake lalle a daukacin lamarin da masu zanga-zangar ke kallon matakin da za a iya dangantawa da a dokesu a hanasu kuka.