1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta gargadi masu neman tayar da fitina a Laberiya

October 16, 2023

Kungiyar ECOWAS ta yi gargadi da kakkausar lafazi kan 'yan takaran shugabancin kasar Laberiya da su guji ikirarin nasara a zaben kasar na ranar 10 ga wannan wata.

https://p.dw.com/p/4XZMc
ECOWAS ta yi kashedi wa masu neman tayar da fitina a Laberiya Hoto: John Wessels/AFP

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi (15.10.2023), kungiyar ta habbaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ta yi gargadin cewar za ta murkushe masu yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar da ta yi kaurin suna a baya wajen rikice-rikice.

Karin bayani: Fargaban faruwar tashin hankali a zaben Laberiya

A dayan hannu kuma ECOWAS din ta ja kunnen masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar, da hukumar zabe da jami'an tsaro kan cewar Tarayyar Afrika da kasashen duniya za su dora masu alhakin duk wani abu da zai haifar da tashin hakali tare da wargaza zaman lafiya a Laberiyar.

Karin bayani: Zaben Laberiya ya dauki hankalin jaridun Jamus

A farkon watan Nowamba mai kamawa ana sa ran zuwa zagaye na biyu a zaben shugaban kasar wanda aka gudanar da zagayen farko cikin rudani da tashe-tashen hankula. 

Tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai da Shugaban kasar mai ci Jeorges Weah su ne manyan 'yan takara a zaben.