Faransa ta yi murnar kawar da Bashar Assad daga mulkin Syria
December 8, 2024Kasar Faransa ta yi maraba da kawar da gwamnatin Bashar Assad da 'yan tawayen HTS suka yi daga kan karagar mulkin kasar Syria, bayan shafe sama da shekaru 10 tana gallazawa al'ummarta da azaba iri-iri.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Christophe Lemoine, ya ce Faransa ta jima tana mika wa Mr Assad tayin tattaunawar sulhunta rikicin kasar, amma ya rinka yin fatali da bukatar.
Karin bayani:'Yan tawaye sun karbe kasar Syria inda shugaba Assad ya arce
Shi ma zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce Bashar Assad ya tsere daga Syria ne bayan da ya rasa goyon baya daga Rasha, yana mai cewar shugaban Rasha Vladimir Putin da ke kare shi ya yi watsi da shi, kamar yadda ya wallafa a shafin na sada zumunta mai suna Truth Social.
Karin bayani:Kusan shekara 12 da barkewar yakin basasa a Siriya
Iran wadda ke dasawa da shugaba Assad, ta sanar da cewa wasu mutane dauke da bindigogi sun far wa ofishin jakadancinta da ke birnin Damascus na Syria.