Nijar: Nasarar sojoji kan 'yan ta'adda
August 25, 2021Tuni al'ummar Jamhuriyar ta NIjar suka fara bayyana gamsuwarsu da wannan nasara da sojojin suka samu kan 'yan ta'addan, tare da yin kira ga gwamnati da ta kara wa dakarun kasar kayan aiki. Sojojin na Nijar sun kaddamar da wannan farmaki ne da suka yi wa lakabi da Billougol de Boni a kan iyakoki uku na Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, a matsayin daukar fansa ga kisan sojojin Nijar 19 da 'yan ta'addan suka yi a wani harin kwantan bauna.
Karin Bayani: 'Yan majalisar jihar Tillaberi sun koka kan tsaro
A ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata ne dai 'ya ta'addan suka kai harin a kauyen Boni na karamar hukumar Torodi, tare da yada hotunan gawarwakin sojojin na Nijar da ma tarin makaman da suka kama a lokacin kazamin harin a shafukan sada zumunta na zamani. Bayanai dai sun tabbatar da cewa tun daga afkuwar wannan lamari zukatan shugabannin sojin Nijar suka fusata, inda suka sha alwashin daukar fansa da kare mutuncin sojoji baki daya.
A kan haka ne suka tsara wannan gagarimin farmaki zuwa maboyar 'yan ta'addan, wanda ya ba su damar fatattakarsu tare da kama motoci da babura da makamai da dimbin man fetur. Da yake tsokaci kan wannan nasarar da sojojin gwamnatin Nijar suka samu kan mayakan 'yan ta'addan shugaban kungiyar ROAD Malam Dambaji Son Allah ya ce, wannan na nuni da irin yadda sojojin ka iya tunkarar matsalar ta'addanci ba tare da goyon bayan sojojin ketare ba.
Karin Bayani: Rashin tsaro da rayuwar yara a Sahel
Wannan nasara da sojojin Nijar suka samu kan 'yan ta'addan ta kasance sahun gaba cikin abubuwan da al'ummar kasar ke tattaunawa, inda kusan kowa ke jinjinawa sojojin da jarumtakar da suka nuna. Wasu bayanai daga jihar Diffa sun bayyana cewa sojojin kasar ta Nijar, sun yi nasarar dakile wani farmaki da mayakan Boko Haram suka kaddamar a garin Baroua da ke da nisan kilomita uku da Tafkin Chadi.